IQNA

Bangaren kasa da kasa; An watsa sabon littafi na Said Muhammad Husein Fadllullah a hankalce da tattaunawa domin kawo canji da sauyi kuma tuni aka buga da watsa wani littafi da cibiyar bugawa da watsa littafai na Bairut ta yi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; An watsa sabon littafi na Said Muhammad Husein Fadllullah a hankalce da tattaunawa domin kawo canji da sauyi kuma tuni aka buga da watsa wani littafi da cibiyar bugawa da watsa littafai na Bairut ta yi. Wannan littafi ne da ked a kima da kuma yake bayyana kan hanyoyin da idan aka yi aiki da su ko shakka babu za a kawo canji da sauyi a cikin al'umma da kuma hakan zai taimaka matuka gaya ko shakka babu ta fuskoki da dama kama daga lamura da suka shafi zamantakewa da siyasa ,akida da addini da sulhu a tsakanin al'ummomin duniya.

684565