IQNA

Matan Saudiya Za Su Samu Cibiyar Bada Horo Tasu Ta Koyar Da Kur'ani

12:00 - November 04, 2010
Lambar Labari: 2025414
Bangaren kasa da kasa; hadin guiwar hardar kur'ani mai girma a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya sun amince kafa cibiyar yada tarbiya da yaye malaman koyar da hardar kur'ani ga mata a wannan kasa.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar kasar Saudiya Alektroniya ya watsa rahoton cewa; hadin guiwar hardar kur'ani mai girma a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya sun amince kafa cibiyar yada tarbiya da yaye malaman koyar da hardar kur'ani ga mata a wannan kasa. Wannan mu'assisar an bata sunan cibiyar koyar da karatu da hardar kur'ani ta Mata kuma wannan it ace cibiya ta farko irin tad a aka amince a gina a kasar ta saudiya kuma an zabi Yusif Almahus daya daga cikin limaman masallatai a birnin Riyad ne aka wakilta a matsayin mai lura da tafiyar da irin wadannan cibiyoyi.


687879

captcha