Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar katari ta Alshark ya watsa rahoton cewa; za a gudanar da bukin girmama wadanda suka gudanar da gasar hadar da karatun kur'ani mai girma a Komoro kuma a ranar sha daya ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya kuma fadar majalisar kasar ce a ka gudanar da wannan buki. A wajen gudanar da wannan buki an samu halaratar manyan jami'ai na gwamnati Komoro day a hada da shugaban kasar ta Komoro da ministoci day an majalisa.
687951