Bangaren kasa da kasa; taro kan kur'ani mai girma da lamarin zamani daga ranar sha tara zuwa ashirin da daya ga watan Esfan na wannan shekara da ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Keniya za ta shirya a jami'ar birnin Nairobi fadar mulkin kasar ta Keniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar al'adu ta Iran a Keniya ya watsa rahoton cewa; taro kan kur'ani mai girma da lamarin zamani daga ranar sha tara zuwa ashirin da daya ga watan Esfan na wannan shekara da ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Keniya za ta shirya a jami'ar birnin Nairobi fadar mulkin kasar ta Keniya. Mahalarta wannan taro za su yi nazari da dogon tunani kan abubuwa da suka shafi addini da kyawawan dabi'u.
694317