Bangaren kasa da kasa;A birin Karbala mai daraja ne aka wallafa da watsa littafi mai suna wazifatul Almajalis Alhuseiniya ma'ana sakon taron zaman Huseiniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Nun ya watsa rahoton cewa; A birin Karbala mai daraja ne aka wallafa da watsa littafi mai suna wazifatul Almajalis Alhuseiniya ma'ana sakon taron zaman Huseiniya.Wannan littafi dai Hasan Kazim Alfatal mawaki kuma masanin adabi a Iraki ya rubuta shi kuma littafin ya kumshi shafuka tamanin da hudu.Mawallafin wannan littafi ya bayyana cewa; wannan littafi dai ya kumshi fasaloli uku ne .Fasalin farko bayani kan muhimmancin da falali gami da amfanonin da ke tattare da ziyartar Imam Husein (AS) yayinda fasali na biyu bincike kan abubuwa da ke sawa kuka don imam Huseini (AS) sai kuma fasali na uku bayani kan muhimmancin gudanar da taron juyayin ranekun shahadar imam Huseini (AS) da kuma sakon da darussan da ke tattare da hakan.
708892