Bangaren kasa da kasa; daga daren sha shidda na wannan wata na azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara na hijira shamsiya a cibiyar Musulunci ta Park 51 a birnin NewYork a guri mafi kusa da gurin da aka kai harin sha daya ga watan satumba za a ci gaba da gudanar da zama da taron juyayin ranekun Muharrama na shahadar Imam Huseini (AS).
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Park 51 ya watsa rahoton cewa; daga daren sha shidda na wannan wata na azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara na hijira shamsiya a cibiyar Musulunci ta Park 51 a birnin NewYork a guri mafi kusa da gurin da aka kai harin sha daya ga watan satumba za a ci gaba da gudanar da zama da taron juyayin ranekun Muharrama na shahadar Imam Huseini (AS). A gurin wannan taro malamai dam asana za su gabatar da bayanai masu gamsarwa da fadakarwa da irin darussan da ke tattare da ashura day a hada muhimmancin Imani, ma'anawiya,dogaro,tsayin daka adalci na zamantakewa.
708417