Bangaren kasa da kasa; kungiyar malaman Palasdinu LPS sun yi kashedi kan tsananta matakan da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ke yi a yankunan da ta mamaye a Kudus musamman a kusa da masallacin Kudus Mai tsarki na kusa masallacin da cewa su tunkari abin da zai biyo baya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labaai ta Palestine Info ya watsa rahoton cewa; kungiyar malaman Palasdinu LPS sun yi kashedi kan tsananta matakan da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ke yi a yankunan da ta mamaye a Kudus musamman a kusa da masallacin Kudus Mai tsarki na kusa masallacin da cewa su tunkari abin da zai biyo baya. A ranar ashirin ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya kungiyar ta malaman Palasdinawa ta fitar da bayani da a cikinsa ta fito karara ta yi kashe da bayyana makircin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke kullawa bayan mamaye Kudus da kuma ruguza masallacin.
711204