IQNA

A Faransa An Gudanar Da Taron Juyayin Ashurar Huseini (AS)

Bangaren kasa da kasa: a ranar alhamis ashirin da biyar ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Saint-Denis na kasar Faransa an gudanar da taron juyayin Ashura ta Shahadar imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da kuma sahabbansa a yankin Karbala'a.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta zinfos974 ya watsa rahoton cewa; a ranar alhamis ashirin da biyar ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Saint-Denis na kasar Faransa an gudanar da taron juyayin Ashura ta Shahadar imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da kuma sahabbansa a yankin Karbala'a. An samu halartar daruruwan ayn shi'a da masoya ahlul baitii (AS) da suka halarci wannnan taro a kan titun Moufia da ke tsakiyar birnin har ila yau an gabatar da jawabai masu gamsarwa ga mahalarta wannan taro na juyayin ashurar Imam Huseini (AS).

713223