IQNA

A Filipin An Gudanar Da Taron Ashurar Huseini (AS)

Bangaren ilimi da nazari: Iraniyawa da sauran musulmi da ke zaune a kasar Pilifine sun gudanar da taron ashura ranar da imam Huseini (AS) ya yi shahada.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Iraniyawa da sauran musulmi da ke zaune a kasar Pilifine sun gudanar da taron ashura ranar da imam Huseini (AS) ya yi shahada. A ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar ta Pilifine ne aka shirya wannan taro kuma da farkon faraway an fara ne da karatun kur'ani mai tsarki da karanto ziyarar ashura sai kuma jawabinda hujjatul islam Azarbaijani ya gabatar dangane da falsafar gudanar da taron ashura.

713576