IQNA

Musulmin Turkiya Suna Adawa Da Tsare Jagoran Musulmin Azarbeijan

Bangaren siyasa da zamantakewa: musulmin kasar Turkiya a ci gaba da nuna adawarsu kan awangaba da tsare Haj Muhsin Samdaf jagoran jam'iyar Islam ta jamhuriyar Aazarbeijan sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar a birnin Istambul da fatar ganin an sako shi.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne daga kasar Turkiya ya watsa rahoton cewa; musulmin kasar Turkiya a ci gaba da nuna adawarsu kan awangaba da tsare Haj Muhsin Samdaf jagoran jam'iyar Islam ta jamhuriyar Aazarbeijan sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar a birnin Istambul da fatar ganin an sako shi.A wajan wannan taron nuna adawa an samu halartar kungiyoyi da shugabannin musulmi da daga da suka halarci gurin wannan zanga-zanga nuna inda suka bayyana adawarsu a fili karara kuma suka bukaci da a sako shi daga inda ake tsare da shi ba tare da wata wata ba.


732701