Bangaren siyasa da zamantakewa: a fadin kasar Indiya za a gudanar da juyayin ranar arba'in na shahadar Imam Huseini (AS) a ranar gobe talata biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.
Kamfanin da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a fadin kasar Indiya za a gudanar da juyayin ranar arba'in na shahadar Imam Huseini (AS) a ranar gobe talata biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. A wajan juyayin wannan rana ta arba'in ga shahadar Imam Huseini (AS) dauke da tutoci masu dauke da sunayen Aba Abdullahi da bayanan zaluncin da aka yi masa .
735056