IQNA

Zaman Tattaunawa Tsakanin Addinan Yahudanci Da Kuma Musulunci A Paris

13:13 - February 28, 2011
Lambar Labari: 2087486
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken tattaunawa tsakanin addinan Musulunci da kuma yahudanci a birnin paris fadar mulkin kasar Faransa, tare da halartar masana daga dukkanin bangarorin biyu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken tattaunawa tsakanin addinan Musulunci da kuma yahudanci a birnin paris fadar mulkin kasar Faransa, tare da halartar masana daga dukkanin bangarorin biyu domin yin bahasi kana bin da suka hadu a kansa.

Bayanin ya ci gaba da cewa zaman taron wanda za agudanar da shi a matasayin na karawa juna sani, zai fara ne daga karfe tara na safe zuwa yamma, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka dukkanin addinan biyu suka hadu a kansu, domin kara samun fahimtar juna tsakanin mabiyansu.

Zaman taron dai zai gudana ne a ginin babbar cibiyar bunkasa al'adu ta Christian peageot dake cikin birnin na paris, daga cikin wadanda za su halarci aman kuwa hard a Kamel Mezitimasanin tarihi da kuma martin Chen, wanda shi kumammasani ne kan harkokin zamantakewa.

za a gudanar da wani zaman taro mai taken tattaunawa tsakanin addinan Musulunci da kuma yahudanci a birnin paris fadar mulkin kasar Faransa, tare da halartar masana daga dukkanin bangarorin biyu.
754560





captcha