Bangaren al'adu da fasaha: an fara kaddamar da sabon zangon koyar da harshen farisanci a birnin Ankara na kasar Turkiya da kuma wannan zangon ya zo a daidai lokacin guda da shiga sabuwar shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an fara kaddamar da sabon zangon koyar da harshen farisanci a birnin Ankara na kasar Turkiya da kuma wannan zangon ya zo a daidai lokacin guda da shiga sabuwar shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in. A wannan zangon koyar da farisanci an bude ajijuwa goma sha biyu ne da dalibai dari daya da sattin da hudu za dauki karatu.
758067