Bangaren fasaha, an jaddada muhimmancin samar da wasu hanyoyi na watsa shirye-shirye a gidajen radiyo domin wayar da kan matasa dangane da harkokin addinin muslunci, ta yadda hakan zai iya amsa tambayoyi da dama da suke da su na rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin masu shirin radiyo Akbar Ashuri ya jaddada muhimmancin samar da wasu hanyoyi na watsa shirye-shirye a gidajen radiyo domin wayar da kan matasa dangane da harkokin addinin muslunci, ta yadda hakan zai iya amsa tambayoyi da dama da suke da su na rayuwa, musamman a wannan zamani da muke ciki.
A bangare guda kuma an gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman taron wanda aka gudanar a birnin Harare, ya samu halartar mutane da suka hada malamai da kuma sauran mabiya a ddinin musulunci mazauna kasar da kuma ‘yan asalin kasar,inda suka saurari bayanai da aka gabatara wajen taron.
An gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidi. 765737