IQNA

An Fara Kasuwar Baje Kolin Rubutun Musulunci A Pakistan

Bangaren kasa da kasa:a ranar goma sha biyar ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ce aka fara gudanar da kasuwar baje kolin nuna iyawa da karewa ta fuskar rubutu a tsakanin musulmi da kasashen musulmi kuma a kasar Pakistan ne ake gudanar da wannan kasuwar baje kolin.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a ranar goma sha biyar ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ce aka fara gudanar da kasuwar baje kolin nuna iyawa da karewa ta fuskar rubutu a tsakanin musulmi da kasashen musulmi kuma a kasar Pakistan ne ake gudanar da wannan kasuwar baje kolin.Wannan gasar nuna rubutu ta kumshi allunna talatin da aka rubuta ayoyin kur'ani mai girma da kuma hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa da kuma addu'o'I da wakokin irfani a cikin harsunan larabci da farisanci.


768572