IQNA

Ana Shirin Fara Gudanar Da Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani Ta Birnin Jiddah

12:08 - April 13, 2011
Lambar Labari: 2105208
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta birnin Jiddah, wadda cibiyar kula da ayyukan kur'ani da shirya gasa ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na ashirin da tara, tare da hadin gwiwa da cibiyar shirya gasa da kasa da kasa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News an habarta cewa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta birnin Jiddah, wadda cibiyar kula da ayyukan kur'ani da shirya gasa ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na ashirin da tara, tare da hadin gwiwa da cibiyar shirya gasa ta duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga tashar rasid an bayyana cewa za a gudanar da wata gasar kuma ta daban, wannan gasa za a gudanar da ita ne a karo na hudu a yankin, inda daruruwan makaranta da kuma mahardata za su kara juna, daga karshe za afitar da sunayen wadanda suka fi nuna kwazo ta fuskacin harda da kuma kira'a, inda za a basu kyautuka na musamman.

Yanzu haka ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki mai take Almarij a yankin Katif, wadda cibiyar kula da shirya gasar karatun kur'ani ta yankin ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da masana daga yankunan gabacin kasar.

773186




captcha