IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Jami’ar Sarki Sa’ud Ta Kasar Saudiyya

18:54 - May 04, 2011
Lambar Labari: 2117547
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur’ani mai tsarki da ta kebanci matasa dalibai da ke karatu a jami;ar sarki a kasar Saudiyya, inda za agudanar da wannan gasa tare da halartar daruruwan dalibai masu sha’awr harkokin kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur’ani mai tsarki da ta kebanci matasa dalibai da ke karatu a jami;ar sarki a kasar Saudiyya, inda za agudanar da wannan gasa tare da halartar daruruwan dalibai masu sha’awr harkokin kur’ani mai tsarki a kasar.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo an bayyana cewa, an gabatar da shawar kafa wani baban kwamiti na marubuta kur’ani mai tsarki da suke kyautata rubutunsa, bayan gudanar da wani zaman taro da aka yi a birnin Madina mai alfarma kan fasahar rubutun kur’ani mai tsarki, wanda ya kawo karshe a ranar litinin da ta gabata tare da halartar marubuta da masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa kafa irin wannan kwamiti zai taimaka matuka wajen karfafa gwiwar masu fasahar rubutun kur’ani mai tsarki su kara mayar da hankali wajen fadada aikin nasu, tare da hada gwiwa wajen kirkiro sabbin hanyoyin gudanar da aikin, kamar yadda hakan ko shakka babu zai karfafa gwiwar wasu masu sha’awa su shiga cikin wannan aiki.
785134
captcha