IQNA

Daruruwan Musulmin Azarbaijan Ne Ke Adawa Da Dokar Hana Sanya Hijabi

Bangaren siyasa da zamantakewa; daruruwan mutane musulmi yan kasar jamhuriyar Azarbaijan ne a marecen ranar juma'ar da ta gabata sha shidda ga watan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya suka gudanar da gagaramar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da kuma dokar da ta kafa ta hana sanya hijabi musamman dokar hana sanya hijabi a makarantun sakandare inda suka yi cincirindo a gaban ma'aikatar koyarwa da tarbiya ta kasar.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; daruruwan mutane musulmi yan kasar jamhuriyar Azarbaijan ne a marecen ranar juma'ar da ta gabata sha shidda ga watan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya suka gudanar da gagaramar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da kuma dokar da ta kafa ta hana sanya hijabi musamman dokar hana sanya hijabi a makarantun sakandare inda suka yi cincirindo a gaban ma'aikatar koyarwa da tarbiya ta kasar.wannan ba shi ne karon farko da musulmin kasar ta Azarbaijan ke nuna adawa da kalubalantar wannan doka ta nuna wariya da karan zana kan musulmi da hana su sanya hijibi a makarantu lamarin day a fito kara ya yi bayani kan yadda gwamnatin jamhuriyar azarbaijan ke baker adawa da addinin musulunci da kuma kan gaba kan baya kan wannan doka da ke fuskantar suka da adawa mai tsananin gasket.


787948