IQNA

Musulmi Su Yi Amfani Da Hanyoyi Na Kimiyya Da Fasahar Zamani

20:03 - August 29, 2011
Lambar Labari: 2178930
Bangaren kur'ani, pira ministan kasar Malazia ya yi kira ga dukkanin musulmi da su yi amfani da fasahar zamani domin bunkasa ilmomin da za su amfanar da al’umamar musulmi na duniya baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Abun ban takaici ne yadda wasu masu kallon kansu a matsayin masana a cikin duniya suke kawo wasu bayanai na rikitarwa dangane da sha'anin kisasi, inda suke bayyana cewa babu hikima a ckin irin wannan hukunci, domin kuwa a ganinsu idan wani ya kashe wani.
Shi kuma aka kashe shi, to mutum biyu aka rasa, kuma wadanda suka kasashe shi su ma sun yi kisan kai. Kuma a cikinsu akwai masu ganin idan aka kashe wanda ya yi kisa, shin wanda aka kashe da farko zai dawo a raye ne? idan har ba zai dawo ba, to a ganinsu babu amfanin a kasha wanda ya kasha shi.
Irin wadannan mutane masu irin wannan karkatattar mahanga, kur'ani ya ba su amsa, inda ya ce rayuwar aminci da salama tana nan cikin kisasi, zartar da hukuncin kisa kan wanda ya yi kisan yana haifar da salama a cikin rayuwar al'umma baki daya.
Wata kila masu irin wannan mahanga suna ganin cewa kisasi tamkar wani aiki ne na daukar fansa ba wai kawai hukunci ne na shari'a ba, alhali idan suka duba a rayuwar duniyar yau, su ka tambayi kansu ina ne inda akafi aikata muggan laifuka na kisa da abin da ya yi kama da haka, za su ga cewa kasashen da ba su yi imani da irin wannan hukuncin ba ne aka fi aikata laifukan kisan kai.
Domin kuwa mai a'aikata irin wannan laifin ya san cewa wata kila zai iya kubuta a kotu, ko kuma hukuncin da zai fuskanta mafi tsanani shi ne a daure shi rai da rai, ko kuma wasu shekaru kamar yadda muke gani yanzu a kasashen da ke da'awar ci gaba.
849914


captcha