IQNA

18:52 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181208
Bangaren kur'ani, an gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki wadda tashar talabijin ta Alkausar ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa da makarancin nan na kasar Masar Izzat Rashid ya zo na daya.Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato labari daga shafin yanar gizo da ke cewa, yanzu haka dai an gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki wadda tashar talabijin ta Alkausar ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa da makarancin nan na kasar Masar Izzat Rashid ya zo na daya a cikin wannan gasa, inda ya samu kyauta ta kimanin dala dubu biyar.

Dukkanin mu mun san cewa a wannan duniya ta mu ta yau da ke cike da ci gaba na masana’antu da sauransu, duk wani abin da wani kamfani ya kera su kan ba wa mai saye takardar da take bayanin dukkanin bangarori na wannan abin, yadda ake amfani da shi da kuma abubuwan da suke cutar da shi, don mai sayen ya san yadda zai yi amfani da shi yadda ya dace don kada ya yi saurin lalacewa.

Ni da ku din nan da kuma dukkanin bil’adama, wata na’ura ce wacce Mahaliccin mu ya halicce mu, sannan kuma sakamakon irin gagarumin rauni na jiki da kwakwalwa da mu ke da shi, mun gaza wajen fahimtar hakikanin kan mu da kuma hanyoyin da za mu sami farin ciki da sa’ada.

A bangare guda kuma shin mu din nan muna kasa da wani firiji ko kuma talabijin ne da wadanda suka samar da su suke ba wa mai saye littafin da ke bayanin yadda za a yi amfani da su, amma kuma Mahaliccin mu ya gagara rubuta wani littafi yadda za mu rayu cikin jin dadi da annashuwa?!!

Ko kuma shin mu din nan bil’adama ba ma bukatar wani littafi mai shiryarwa wanda a cikinsa aka yi karin haske dangane da siffofin da jiki da ruhin mu ya kebanta da su haka nan kuma da irin karfi da damar da muke da shi? Ko kuma hanyar da ta dace wacce za a bi wajen amfani da irin wannan karfi da kwarewa da muke da su ba.

852695

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: