IQNA

Yada Fahimtar Kur'ani Na Daga Muhimman Ayyukan Isar Da Sako

17:10 - September 15, 2011
Lambar Labari: 2187787
Bangaren kasa da kasa, yada sakon addinin muslunci na daga cikin muhimman ayyuka na masu isar da sakon addinin muslunci a duniya, domin kuwa ta hanayar fahimtar kur'ani mai tsarki da sakon da yake dauke da shi ne za a iya fahimtar hakikanin sakon muslunci.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na makarantar Ali-Imran a birnin Lahur na kasar Pakistan cewa, yada sakon addinin muslunci na daga cikin muhimman ayyuka na masu isar da sakon addinin muslunci a duniya, domin kuwa ta hanayar fahimtar kur'ani mai tsarki da sakon da yake dauke da shi ne za a iya fahimtar hakikanin sakon muslunci ga sauran al'ummomi.

Bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurnin manzon Allah a lokacin yakin Uhud, wasu daga cikinsu zuciyarsu ta raunana, sai suka fara jin tsoro, suka fara nuna damursu da kaduwarsu a fili, suna tambayar cewa yaya makomarsu za ta kasance idan kafirai suka yi nasara a kansu, kenan za su kaskanta.

A cikin nassin wannan aya mai albarka Allah madaukakin sarki yana sheda ma manzonsa (SWA) cewa nasarar da kafirai suka samu a Uhud bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurninsa, ba nasara ce ba ga kafirai, haka nan kuma ba wata daukaka ba ce balantana su daga ma musulmi kai, hakan lamari ne kawai da zai kara saka su cikin halakar kafirci da shirka, suna cikin hasarar duniya da kuma hasarar lahira.

Haka nan kuma kafircin wadannan mushrikai ba zai cutar da Allah madaukakin sarki da komai ba. Maimakon haka ma su ne suke cutuwa da kafirci da shirkarsu, kuma su koma zuwa ga Allah su shiga azaba mai radadi.
858756

captcha