Bangaren kasa da kasa:A karo na ashirin da hudu an fara gasar karatun kur'ani da hadisai ta kasa da kasa musamman ga matasa daga kasashen yankin tekun fasha kuma a jiya ne hudu ga watan Mehr shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gasar da za a kwashe kwanaki hudu a jeer ana gudanarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; A karo na ashirin da hudu an fara gasar karatun kur'ani da hadisai ta kasa da kasa musamman ga matasa daga kasashen yankin tekun fasha kuma a jiya ne hudu ga watan Mehr shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gasar da za a kwashe kwanaki hudu a jeer ana gudanarwa. Yusuf Alsa;idi shugaban komitin shirya wannan gasar ta kur'ani ne ya bayyana cewa: hukumar shirya wasa da kuma kula da sha'anin matasa ta kasar Koweiti ce ta shirya da zummar bawa matasa daga kasashen yankin tekun fasha damar halarta a fannoni guda biyu na kur'ani da kuma hadisi.
867306