IQNA

Sai An Doki Zanan Yatsar Maniyata Hajji A Bana

Bangaren kasa da kasa; a bana duk wani Mahajjati sai an doki zanan yatsarsa kafin ya fara gudanar da ayyukan sabke faralin hajji.


Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a bana duk wani Mahajjati sai an doki zanan yatsarsa kafin ya fara gudanar da ayyukan sabke faralin hajji.Mahukumtan Saudiya sun fake da cewa wannan mataki sun doke shi ne domin gano wadanda suke shiga biranan makka da madina ba tare da izinin ba.Janar Ayid bin Tgalib shugaban ofishin da ke bayar da vizar hajji dangane da wannan lamari ya bayyana cewa: duk wani mahajjaci da ked a niyar sabke farali a bana sai an doki hoton zanan yatsarsa inda ya kara da cewa; duk wani mataki fara wannan aiki ya kammala kuma an sanya a filin sabka da tashin jirage na Jidda da Madina.


880597