IQNA

Tsari Da Yawan Wadanda Suka Halarci Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa

14:29 - October 24, 2011
Lambar Labari: 2210903
Bangaren harkokin kur'ani : mukaddashin hukumar da ke kula da al'adu da harkokin addini a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya jinjinawa wadanda suka shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa karo na ashirin da takwas da cewa; a wannan karo an samu karuwar wadanda suka halarci wannan gasar da kuma tsarin gudanarwa Allah san barka.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mukaddashin hukumar da ke kula da al'adu da harkokin addini a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya jinjinawa wadanda suka shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa karo na ashirin da takwas da cewa; a wannan karo an samu karuwar wadanda suka halarci wannan gasar da kuma tsarin gudanarwa Allah san barka.Hujjatul Islam walmuslim Ahmad Sharaf Khani mukaddashin hukumar da ke kula da al'adu da harkokin addini a nan jamhuriyar musulunci ta Iran a ranar daya ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani bukin jinjinawa wadanda suka shirya wannan gasar ya bayyana gamsuwarsa da tsarin da cewa: wakilai daga kasashe sattin da daya ne na musulmi da wadanda ba muslmi ba suka halarci wannan gasar ta kasa da kasa inda aka yi fafatawa mai zafi a tsakanin yan takarar da hakan ke nuni da yadda gasar ta samu karbuwa da tsari mai kyau da karuwa wadanda suka halarci gasar.


885326

captcha