Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an tarjama littafin Hikaye Payambaran be Ruwayate Kur'ani a cikin harshen Jamusanci da Abu Hasan Ali Alhasani Alnadwa ya rubuta kuma tuni a shigar da shi a cikin kasuwa ga mai bukata .Kissar rayuwar Annabawa shi ne bangare da yafi yawa da wannan littafi ya kumsa domin zama darasi da abin koyi a rayuwarmu ta yau da kullum har ila yau akwai tarihi da kisssar mala'iku da dai sauran abubuwan na kissoshin annabawa da suka zo a cikin kur'ani mai girma.
886667