Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokacin shigar Muharram mu'assisar kur'ani a Iraki ta shirya wasu shirye-shirye iri-iri na kur'ani da suka hada da gasar karatun Kur'ani mai girma da kuma jawabai da azadari na tarbar watan Muharram.Ra'ad Adnan Shazar Alnasiri mai hulda da jama'a a komitin koli na kur'ani mai girma da ke karkashin tawagar ministoci Iraki a lardin Zi Kar da kuma shugaban mu'assisar Darul Kur'ani a garin Alnasiriya a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya bayyana cewa sun shirya tarbar watan muharram tare da shurya shirye masu gamsarwa.
904854