IQNA

Mata Mahardata Kur'ani Iraniya Sun Ziyarci Darul Kur'anul Karim A Karbala

16:34 - December 07, 2011
Lambar Labari: 2234975
Bangaren kasa da kasa: wata tawaga ta mata mahardata kur'ani Iraniyawa sun ziyarci darul Kur'anul Karim da ke karbala a ranar sha biyu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya domin yin masanyar kwarewa da fahimta a tsakanin takwarorinsu na Darul Kur'anil Karim a yanki mai tsarki na imam Huseini (AS) a karbala.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wata tawaga ta mata mahardata kur'ani Iraniyawa sun ziyarci darul Kur'anul Karim da ke karbala a ranar sha biyu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya domin yin masanyar kwarewa da fahimta a tsakanin takwarorinsu na Darul Kur'anil Karim a yanki mai tsarki na imam Huseini (AS) a karbala.A wannan ziyarar gani da idon kimanin mata arba'in ne mahardata kur'ani a mu'assisar koyar da kur'ani mai tsarki ta Mah Kur'ani a yankin Kazvin na kasar Iran suka samu sa'ar ziyartar wannan yanki domin ganewa idonsu yadda mata takwarorinsu ke yin harder kur'ani a Karbala.

910931

captcha