IQNA

Makomar Duniya Tana Ga Musulunci Ne

Bangaren kasa da kasa: Sheikh Khalid Yasin wani malami musulmi dan kasar Amerika a cikin wani jawabi da ya gabatar a masallacin Sultan Kabus a Maskat babban birnin kasar Oman ya bayyana cewa; makomar duniya tana komawa ne ga musulunci.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa' Sheikh Khalid Yasin wani malami musulmi dan kasar Amerika a cikin wani jawabi da ya gabatar a masallacin Sultan Kabus a Maskat babban birnin kasar Oman ya bayyana cewa; makomar duniya tana komawa ne ga musulunci.Kamar yadda aka nakalto daga jaridar Oman Observer Yasin da farko ya kasance kirista kafin ya zama musulmi a shekara ta dubu daya da dari tara da sattin da biyar kuma ya gabatar da jawabai da lakcoci ne daga ranekun sha shida zuwa sha takwas ga watan azar na shekara ta dubu daya da darin uku da tis'in hijira shamsiya a masallacin Sultan Kabus inda ya kawo hujjoji da bayanai masu gamsarwa kan makomar duniya tana ga musulunci ne.

912421