Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : Allah madaukakin sarki day a sabkar da kur'ani a kirjin ma'aikinsa Annabin rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a agre shi da alayan gidansa domin shiryar da al'umma da kawo gyara a tushen tunani da tsarin mutum to shi ma tsayuwa da gwagwarmayar Imam Huseini (AS) a ranar ashura domin kawo gyara ne a cikin al'umma da tunan mutum saboda haka abubuwa guda biyun nan Kur'ani da waki'ar Ashura sun hadi kan buri daya.Mahan Aladil wani marubuci manazarci kan kur'ani dan kasar Iraki a cikin wata makala day a rubuta mai sunan daga Kur'ani zuwa Huseini (AS) da tsari tabbatacce yayi wannan bayani da kawo hujjoji gamsarsu da ke tabbata da abun day a fada da hadewar abubuwa biyu wato kur'ani da gwagwarmayar Imam Huseini (AS) a ranar waki'ar ashura kan buri daya na shiryar da intar da al'umma ta hanayr daura ta kan tafarkin gaskiya da shiriya.
913724