Bangaren kasa da kasa: sojojin da jami'an tsaro na gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila a ranar ashirin da daya ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun dakilai da rufe kofar shiga gadar babul magariba da ke isa ga masallacin Kudus mai tsarki a matakan da gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila ke dauka na zalunci.
Kamfanin dillancin labarai na ikana da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: sojojin da jami'an tsaro na gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila a ranar ashirin da daya ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun dakilai da rufe kofar shiga gadar babul magariba da ke isa ga masallacin Kudus mai tsarki a matakan da gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila ke dauka na zalunci.Mai Magana da yawun jami'an yan sanda na gwamnatin zalunci a aharamtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana cewa: karkashin umarni daga magajin yahudawan sahayoniya a garin kudus kuma a fadarsa dimin kare rayukan al'umma ne suka dauki matakin rufe wannan mashiga ta gadar sai dai kowa ya san karya suke yi domin kuwa sun jima suna kokarin rufe wannan mashiga domin hana Palasdinawa samin damar zuwa masallacin Kudus da kuma karkata tarihi da abubuwa na tarihi a yankin.
914740