IQNA

Tutar Palasdinu Ta Kada A Hedkwatar Yunusco

Bangaren kasa da kasa: tutar Palasdinu ta kada a hedkwatar hukumar kula da ilimi da al'adu a duniya ta Yunesco ta majalisar dinkin duniya da ke a birnin Paris na kasar faransa a ranar ashirin da biyu ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma an gudanar da burin a musamman a daidai lokacin daga tutar palasdinun a wannan hedkwata.



Kamfanin dillancin labarai na ikana da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: tutar Palasdinu ta kada a hedkwatar hukumar kula da ilimi da al'adu a duniya ta Yunesco ta majalisar dinkin duniya da ke a birnin Paris na kasar faransa a ranar ashirin da biyu ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma an gudanar da burin a musamman a daidai lokacin daga tutar palasdinun a wannan hedkwata.Bayan wata guda da amincewa da Palasdinu a matsayin kasa a jiya ne aka daga tutar Palasdinu a wannan hedkwata ta hukumar Yunesco mai kula da ilimi da al'adu a duniya a wani mataki na jinjinawa ga hukumar da ta dauki wannan mataki duk da cewa ta fuskanci matsin lamba da suka mai tsanani daga kasar Amerika mai martabawa haramtacciyar kasar Israila baya. Kuma a wanio matakin ladabtar da hukumar gwamnatin Amerika ta janye irin taimako na kudi da take bawa wannan hukumar a ci gaba da adawar da take nunawa kan wannan mataki da hukumar ta dauka .A wajan wannan buki an samu halaratra manyan yan siyasa da shugabanni da wakilan palasdinawa kamar Mahmud Abassa shugaban gwamnatin kwarya kwarya ta palasdini da jami'an hukumar ta Yunesco da jakadun kasashe da ke manbobi a hukumar.

914703