Bangaren harkokin kur'ani : an kawo da kammala taron kasa da kasa kan kur'ani da kuma rawar da kur'ani ya taka wajan gina dan adam da wayewarsa kuma an gudanar da wannan taro na kasa da kasa domin tunawa da cika karni goma sha hudu da sabkar kur'ani mai girma kuma jami'ar kasa da kasa ta Afrika da ke birnin Kratum fadar mulkin kasar Sudan ne aka shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula d aharkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an kawo da kammala taron kasa da kasa kan kur'ani da kuma rawar da kur'ani ya taka wajan gina dan adam da wayewarsa kuma an gudanar da wannan taro na kasa da kasa domin tunawa da cika karni goma sha hudu da sabkar kur'ani mai girma kuma jami'ar kasa da kasa ta Afrika da ke birnin Kratum fadar mulkin kasar Sudan ne aka shirya.A wajan wannan taron an samu halartar masana da malaman addini da musulmi da daman gaske da kuma gabatar da jawabai masu gamsarwa kamar yadda Ali Usman Muhammad Daha mukaddashin shugaban kasar Sudan na farko a cikin jawabin bude wannan taro ya nemi uzirin mahalarta taron kan rashin halartar shugaban kasar ta Sudan wanda aka shirya shi ne zai bude taron ya kuma yiwa mahalarta taron kimanin dari hudu maraba da zuwa da halartar wannan taro mai matukar muhimmanci.
918592