IQNA

Taron Binciken Matsalolin Da Ake Fuskanta A Tarjama Kur'ani Da Sauran Yaruka

16:37 - December 21, 2011
Lambar Labari: 2243017
Bangaren kasa da kasa; a karo na hudu na jerin tarukan da ake gudanarwa na binciken irin matsalolin da ake fuskanta a lokacin tarjama kur'ani mai girma a cikin yaruka da kuma a wannan karo aka bawa taken bincike da sanin irin matsalolin da ake fuskanta a cikin tarjamar kur'ani da kuma yin dubu a cikin wasu yarukan da kuma za a fara taron a yau.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : a karo na hudu na jerin tarukan da ake gudanarwa na binciken irin matsalolin da ake fuskanta a lokacin tarjama kur'ani mai girma a cikin yaruka da kuma a wannan karo aka bawa taken bincike da sanin irin matsalolin da ake fuskanta a cikin tarjamar kur'ani da kuma yin dubu a cikin wasu yarukan da kuma za a fara taron a yau.Wannan taro dai na hadin guiwa ne tsakanin kamfanin dillancin labarai na Ikna da kuma jami'ar kula da ilimin addini da sanin kur'ani mai girma kuma da misalign karfe biyu da rabi na ranar ashirin da tara ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gudanar da wannan taro na binciken matsalolin da ake cin karo da su a lokacin tarjama kur'ani.A lokacin wannan taro na bincike masu tarjama a cikin rayuka daban daban na duniya ne suka yi bayani kan irin matsalolin da suke fuskanta alokacin da suke tarjama kur'ani a cikin yarukansu kamar yaren Espaniyanci .

919230

captcha