IQNA

An Bukaci Tara Kur'anai Da Ke Ajiye A Gidajai A Masar Domin Kai Su Kasashen Afrika

10:26 - December 26, 2011
Lambar Labari: 2245285
Bangaren kasa da kasa; mu'assisar aiwatar da ayyukan alheri Yumna da ke kasar Masar ta fitar da wani bayani na yin kira da babbar murya da al'ummar kasar da su bayar da kyautar kur'anai da suke ajiye a gidajensu da ba su amfani da shi domin kai su kasashen kuduncin Afrika.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mu'assisar aiwatar da ayyukan alheri Yumna da ke kasar Masar ta fitar da wani bayani na yin kira da babbar murya da al'ummar kasar da su bayar da kyautar kur'anai da suke ajiye a gidajensu da ba su amfani da shi domin kai su kasashen kuduncin Afrika.Idan aka tarrara wadannan kur'anai a kasar ta Masar da kuma kais u kasashen kuduncin Afrikan za a ajiye su a masallatai domin yin amfani da su da karanta su a masallatai da hakan zai amfanar da mutane da samin falala da kuma samin lada mai yawan gaskie.Akwai irin wannan kungiya da dama a kasashen larabawa da na musulmi da ke gudanar da irin wannan aiki na taimakawa al'ummar ta littafai da abincin da shad a kuma sutura da kuma wannan aiki ke zama daya daga cikin hanyoyin taimakawa maras shi da galihu .

922190

captcha