Bangaren kasa da kasa:cibiyar kur'ani da ke karkashin kulawar hadin kan musulminyan asalin kasar Indiya mazauna kasar Katar sun fitar da wata sanarwa da ta shafi gasar kur'ani da suke gudanarwa a fadin kasar ta katar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ikna ne ya watsa rahoton cewa; cibiyar kur'ani da ke karkashin kulawar hadin kan musulminyan asalin kasar Indiya mazauna kasar Katar sun fitar da wata sanarwa da ta shafi gasar kur'ani da suke gudanarwa a fadin kasar ta katar.A jiya juma'a sha shidda ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a makarantar Indiya mai suna Shantiniktan da ke birnin Doha fadar mulkin kasar katar aka gudanar da wannan gasar kuma kimanin makaranta kur'ani dari uku da saba'in ne suka halarci wannan cibiyar domin halartar wannan gasar ta karatun kur'ani da ta tattaro makaranta kur'ani yan asalin kasar Indiya mazauna kasar ta Katar.
929857