Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Komandan hadin guiwar sojojin tarayyar Nigeria JTF ya karyata labarin da ake yadawa a yan kwanakin nan wai wani daga cikin sojojin kasar ta Nigeria ya wulakanta kur'ani mai girma.An nakalto daga jaridar Nigerian Tribune cewa janar Vitor Anhalam ya fitar da wani bayani da a cikinsa yak e karya labarin da ake yadawa a yan kwanakin nan wai wani daga cikin rundunar sojin kasar ya ci fuska da wulakanta kur'ani mai girma kuma ya kara da cewa sun gudanar da cikekken bincike kan wannan lamari kuma sun gamsu da fahimtar karya ce kawai aka yada . Har ila yau wannan jami'in soja ya kara da cewa : wannan raderadi ya fito ne daga bangaren kungiyar nan da ake kira book haram da ke fafatawa da fito na fito da jami'an gwamnatin kasar ta Nigeria.
936514