IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani A Fadin Hadeddiyar Daular Larabawa

15:39 - January 21, 2012
Lambar Labari: 2260667
Bangaren kasa da kasa; a karo na uku za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da harda a fadin hadeddiyar daular larabawa a gasar da aka bawa sunan kyautar kur'ani ta Khalifa bin Jabir da kuma za a fara a ranar shida ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na uku za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da harda a fadin hadeddiyar daular larabawa a gasar da aka bawa sunan kyautar kur'ani ta Khalifa bin Jabir da kuma za a fara a ranar shida ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya. Wannan gasar cibiyar da ke kula da harda da karatun kur'ani ta Abu Zabi ce tashirya karkashin sa idon babbar tawagar da ke kula da harkokin addini a Hadeddiyar daular larabawa.Wannan gasar ta kumshi juz'I na ashirin da kuma harda juzi na sha biyar da kuma goma har ila yau na kuma na biyar da na uku da kuma juz'I na biyu .Har ila yau a dabra da haka akwai gasar karatun kur'ani da aka ware ga masu rashin lafiya na musmamman .
938259

captcha