Bangaren kasa da kasa:a karo na shidda a garin karbala mai tsarki za a gudanar da taron baje kolin abubuwa da suka shafi kur'ani mai tsarki da abubuwan addini da aka bawa taken rabi'ul Risala wato damunar sakon annabci kuma ana gudanar das hi a daidai wannan lokaci na zagayowar ranekun tunawa da ranar haifuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa da kuma Imam Jafar Sadik (AS).
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na shidda a garin karbala mai tsarki za a gudanar da taron baje kolin abubuwa da suka shafi kur'ani mai tsarki da abubuwan addini da aka bawa taken rabi'ul Risala wato damunar sakon annabci kuma ana gudanar das hi a daidai wannan lokaci na zagayowar ranekun tunawa da ranar haifuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa da kuma Imam Jafar Sadik (AS).Wannan kasuwar baje kolin za a fara ta ne a ranar sha tara ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zuwa ranar ashirin da daya ga watan bahman a daidai wannan lokaci na tunawa da ranar tunawa da zagayowar ranar mai muhimmanci da daukaka ta haifuwar fiyayyan halitta Muhammad dan Abdullahi ma'aikin Allah tsira da aminicin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka wanda aka yi duniya da lahira don shi.
944970