Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karon farko za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da makarantar musulunci ta Almahdi ta shirya a lardin Pansilvaniya na kasar Amerika. Wannan gasar ta shafi yara yan sheakara hudu zuwa shidda da za su karato surori na Fatiha,Ma'un,Kafirun, Masad ,Falaki da nasi sai kuma yara daga shekaru bakwai zuwa sha daya da hafuwa da za su karanto sororin: Shams,Duha,Sharh,Alak ,Zilzila da Adiyat t=yayin das u kuma yan shekaru sha biyu zuwa sha shida za su karanto surorin Naba',Mudafifina ,Buruj ,Gashiya,Balad da Fajr.
956807