Kamfannin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani ami girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ministan harkokin wajan kasar Jamus bayan ya yi Allah wadai da babbar murya kan kona kur'ani mai girma da wasu sojojin Amerika suka yi a cibiyar sojojin Amerika Bagram da ke arewacin Kabul babban birnin Afganistan wani aiki mai muni kona kur'ani mai girma. Bayan an nakalto daga muryar Afganistan Ava an watsa rahoton cewa: bangaren da ke kula da harkokin labarai a fadar shugaban kasar Afaganistan ta bayyana cewa: Gido Waster Vela ministan harkokin wajan kasar Jamus a ta wayar tarho ya tattauna da Rangin Dadfar Sinta mai kula da harkokin tsaron kasa a Afganistan ya bayyana masa damuwarsa da yadda aka ci mutuncin littafin mai daraja na musulmi kuma abin yin Allah wadai ne kuma wannan wani babban abin yin Allah wadai ne.
961138