Bangaren kasa da kasa: ministan da ke kula da harkokin addinin musulunci a Palsdinu a ranar tara ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya soki fatawar da shugaban kungiyar hadin kan malumai muslumi na duniya da ya fitar da fatawar haramta ziyartar kudus mai tsarki ga wanda ba bapalsdine bad a cewa wannan fatawa ta sabawa kur'ani da sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ministan da ke kula da harkokin addinin musulunci a Palsdinu a ranar tara ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya soki fatawar da shugaban kungiyar hadin kan malumai muslumi na duniya da ya fitar da fatawar haramta ziyartar kudus mai tsarki ga wanda ba bapalsdine bad a cewa wannan fatawa ta sabawa kur'ani da sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa.Jaridar aldastur da ake bugawa a kasar Masar ta buga labarin cewa: Mahmud Alhabash ministan kula da harkokin addini a Palsdinu ya bayyana cewa; fatawar da Yusuf Kardawi shugaban hadin kan malamai musulmi na duniya ta haramta ziyaratar birnin Kudus mai tsarki ga wanda ba Bapalsdine ne ya sabawa kur'ani da sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka kuma ziyartar Kudus wani nauyi ne na sharia kuma larura c eta siyasa kuma wani hakki ne da duk wani musulmi da babu wanda ya isa ya kwace masa wannan hakki. Mahmud Alhabash ya ci gaba da cewa; yana bukatar Kardawi day a janye wannan fatawa tasa domin wanna fatwa kuskure ne kuma a fili ta sabawa kur'ani da hadisin ma'aikin Allah kuma wata hidima ce kyauta hankali kwance yayi way an mamaya haramtacciyar kasar Isra'ila da ke son fitar da Kudus daga ikon larabawa da musulmi.
962952