IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Munin Kona Kur'ani A Afganistan

12:36 - March 01, 2012
Lambar Labari: 2283615
Bangaren harkokin kur'ani : a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan ne aka gudanar da wani taron karawa juna sani kan munin kona kur'ani kuma a ranar tara ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka gudanar da wannan taro karkashin kulawar cibiyar da ke kula da al'adu da yada addinin musulunci karkashin koyarwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a kasar Afganistan.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan ne aka gudanar da wani taron karawa juna sani kan munin kona kur'ani kuma a ranar tara ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka gudanar da wannan taro karkashin kulawar cibiyar da ke kula da al'adu da yada addinin musulunci karkashin koyarwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a kasar Afganistan. A gurin wannan taro an samu halartar malamai addinin musulunci masu yawan gaske da jagorori da shugabannin siyasa da na kungiyoyin al'umma da na addini da suka halarci wannantaro kuma an gabatar da jawabai masu gamsarwa kan munin kona kur'ani ko kuma mataki makamancin haka da kuma nauyi day a rataya kan musulmi a duk inda yak e na tunkarar wannan lamari mai muni na kaskantar da musulmi da addininsu na musulunci da ke bawa mutunta juna da sauran al'ummomi hatta wadanda ba musulmi ba muhimmanci da kuma mutunta littafai da addini kowa ba tare da izgili ko tsangwama ba. Mahalarta taron sun yi Allah wadai da yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar afganistan suka kona wasu kur'anai wuta a wani mataki na takalar fada da neman izgili.


962698
captcha