IQNA

Matakin Baya Bayan Nan Na Amerika Kan Kur'ani Ya Karawa Mutane Rungumar Kur'ani

12:35 - March 01, 2012
Lambar Labari: 2283618
Bangaren siyasa : ministan al'adu da fadakarwa irin ta musulunci a jiya ne goma ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a gaban manema labarai ya yi nuni da cin mutuncin kur'ani mai girma da wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka yi da cewa; musulmin za su maida martini mai tsanani kan wannan mummunan aiki kuma mutane sun kara rungumar kur'ani ne.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ministan al'adu da fadakarwa irin ta musulunci a jiya ne goma ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a gaban manema labarai ya yi nuni da cin mutuncin kur'ani mai girma da wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka yi da cewa; musulmin za su maida martini mai tsanani kan wannan mummunan aiki kuma mutane sun kara rungumar kur'ani ne.Said Muhammad Huseini ministan kula da harkokin al'adu da fadakarwa ta musulunci a daidai lokacin day a ke bada amsar tambayar da aka yi masa a wani taron manema labarai na ikna kan martanin day a dace a mayar kan cin mutuncin kur'ani mai girma da wasu sojojin Amerika a Afganistan suka yi ya bayyana cewa: gaskiya ne al'ummar Iran a yau ta maida hankali kan zaben yan majalisar dokoki amma wadanda ke bin diddigin wannan lamari sun mayar da martini da yin Allah wadai kuma wannan ba wani sabon abu ba ne ga Amerika dama ta saba kuma wannan ne zai sa a kara tsanarta a yankin fiye da da.
962878
captcha