IQNA

Taron Birnin Madrid Na Binciken Fadakar Musulmi A Yau

Bangaren siyasa da zamantakewa; a birnin Madrid na kasar Spain ne aka gudanar da wani taro na masana da kwararru da kuma malamai da marubuta a ranar sha biyu ga watan Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jami'ar Kambalotansa na birnin kuma taron ya kumshi bincike da nazari kan fadakar musulmi a yau da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare ya shirya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a birnin Madrid na kasar Spain ne aka gudanar da wani taro na masana da kwararru da kuma malamai da marubuta a ranar sha biyu ga watan Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jami'ar Kambalotansa na birnin kuma taron ya kumshi bincike da nazari kan fadakar musulmi a yau da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare ya shirya.A wannan taron na binciken fadakarwar da musulmi suke yi a yau ya hada masana da manazarta da malaman jami'o'I da daliban jami'a kimanin dari da hamsin . Amir Purpazeshk mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Spain a jawabin day a gabatar ya bayyana cewa; ana samin gagaramin sauyi mai fadi a yankin kamar abubuwan da suka faruwa a na rikici da zanga zanga a Bahrain da yadda ake kirayekirayen a aiwatar da adalci a yau da kawo karshen zalunci da azzalumai a yankin da kuma irin danniyar da ake yiwa musulmi a yankin.
964026