Bangaren siyasa: za a shirya wani taro na samar da hanyoyi da salon tunkara da fuskantar duk wani mataki na cin mutuncin kur'ani mai giram ada makiyan musulmi ke yi da kuma kawo karshen irin wanna cin zarafi da makiya masu son takalar fada da haddasa fitina kan musulmi ke yi kuma a gurin wannan taron za a samu halartar hujjatul Islam Hamid Mahmudi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: za a shirya wani taro na samar da hanyoyi da salon tunkara da fuskantar duk wani mataki na cin mutuncin kur'ani mai giram ada makiyan musulmi ke yi da kuma kawo karshen irin wanna cin zarafi da makiya masu son takalar fada da haddasa fitina kan musulmi ke yi kuma a gurin wannan taron za a samu halartar hujjatul Islam Hamid Mahmudi. A yau ne sha biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da misalin karfe goma da mintoci talatin agogon nan jamhuriyar musulunci ta Iran aka bude taron a hedkwatar kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran kuma a gurin wannan taron mahalara taron za yi dogon nazari da hangen nema kan yadda za su kawo karshen wannan cin kasha da cin zarafi da makiya ke nuna wa abubuwa masu daraja da daukaka na musulmi .Kuma masu halartar wannan taron sun fara ne da yin Allah wadai da cin zarafin kur'ani mai tsarki da wasu sojojin mamaye na amerika suka yi ta hanayar kona kur'anai a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan.
965314