Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mana alkalai a kotun kolin garin Lahur na kasar Pakistan sun yi Allah wadai da tofin Allah tsine da cin mutunci da cin fuska da waso sojojin mamaye na Amerika a Afganistan suka yi a birnin Kabul fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Afganistan. Har ila yau alkalan a wannan kotun koli ta birnin Lahur sun bukaci gwamnatin Pakistan da ta yi Allah wadai da wannan mummunan aikin sojojin Amerika a kasar Afganistan da ta shigar da karar Amerika a gaban majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi domin bin diddigin hakkokin musulmi da daukan mataki na hukumta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki na kona kur'ani mai tsarki da sojojin Amerika a Afganistan da kuma hakan ya sa a dauki mataki hana abkuwar irin wannan danyan aiki.
965259