Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an wanna karni na kur'ani da kuma na ma'anawiya da kuma ke bukatuwa ga komawa ga kur'ani ana bukatar fadada yawan labarai da harsunan da kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ke yi.Muhammad Huseini Abidini mai kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Karkazistan a wata tattaunawa day a yi da Ikna dangane da bude shafin labarai na kamfanin cikon na arba'in ya bayyana cewa; karkashin albarakar kur'ani mai girma da niyar shugabanni da ma'aikatan wannan kamfani a tsawon shekaru takwas na ayyukan da suke gudanarwa a wannan bangare na Internet sun aiwatar da ayyuka masu kyau kuma gamsassu mnasu kayatarwa . ya kara da cewa; a yau wannan kamfani ya bunkasa da kaiwa ga kamala ta inda yana watsa labarai da suka shafi kur'ani mai girma da kuma yada harkokin addini a cikin yaruka da harsuna arba'in na duniya kuma a duk lokacin da aka fadada nau'I da yawan labarai na kur'ani a wannan karni zai taima wa al'ummomi na musulmi da wadanda ba musulmi ba wajan sanin hakikanin addinin musulunci da kur'ani mai girma da kuma hakan zai kara karfin ma'anawiya a tsakanin al'ummomi da mutane a fadin duniyar nan .
969734