IQNA

A Jiya Ne Aka Gudanar Da Taron Manema Labarai kan Gasar Kur'ani Ta Kasar Katar

12:14 - March 14, 2012
Lambar Labari: 2291726
Bangaren kasa da kasa; a jiya ne ashirin da uku ga watan Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya komitin shirya gasar karatun kur'ani mai girma ta Sheikh Jasim Bin Muhammad Al Sani karo na sha tara a fadin kasar da za a fara a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar.



Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a jiya ne ashirin da uku ga watan Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya komitin shirya gasar karatun kur'ani mai girma ta Sheikh Jasim Bin Muhammad Al Sani karo na sha tara a fadin kasar da za a fara a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar.Jaridar Alshark da ake bugawa a kasar Katar ta buga cewa a wannan taron manema an bayyana lokacin gudanar da wannan gasar ta karatun kur'ani mai girma da kuma fara rubuta sunayen makaranta da mahardata kur'ani da kuma dokokin shiryawa da tsarin gudanar da wannan kasar ta karatun kur'ani ta Sheikh Jasim bin Muhammad Ali sani a shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku hijira kamariya. Kamar yadda aka tsara Said Muhammad Mahmud Almahmud shugaban komitin shiryarwa sai kuma Nasir Yusuf Alsalaiti mataimakin shugaban komitin.

971172
captcha