IQNA

Dole A Yi Hukumci Mai Tsanani kan Sojojin Amerika da Suka Gona Kur'anai

15:34 - March 18, 2012
Lambar Labari: 2293587
Bangaren siyasa da zamantakewa; mukaddashin babbar cibiyar rundunar sojin sama na jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; dole a dauki mataki da hukumta sojojin Amerika da suka kona kur'ani mai girma a kasar Afganistan hukumci mai tsanana kuma dole ne hukumcin da za a yi masu ya kasance a cikin kasar ta Afganistan domin ya zama babban darasi ga sauran.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mukaddashin babbar cibiyar rundunar sojin sama na jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; dole a dauki mataki da hukumta sojojin Amerika da suka kona kur'ani mai girma a kasar Afganistan hukumci mai tsanana kuma dole ne hukumcin da za a yi masu ya kasance a cikin kasar ta Afganistan domin ya zama babban darasi ga sauran. Janar Said mas'ud Jaza'iri ya yi bayani dalla dalla da cewa; ko kusa musulmi ba za su yafe ba ko manta wannan mummunan aiki na sojojin mamayen Amerika karkashin kungiyar tsaro ta nato a Afganistan domin wannan bas hi ne karon farko da suke muzunta kur'ani mai girma da yi wa abubuwa masu kima da daraja na musulmi rikon sakainar kasha kuma matukar ba hukumta sojojin Amerika da suka aikta wannan aiki hukumci mai tsanani kuma a cikin kasar ta Afganistan to ko shakka babu fushi da musulmi kr ciki bas u su yi shayi ba.Har ila yau ya kara da cewa hukumta sojojin Amerika da suka aikata wannan aiki a kasar Afganistan ne tare da neman afuwar musulmin duniya zai sa su fahimci wannan lamari idan kuwa ba haka ba musulmi za su ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da wannan aiki da kuma ganin a hukumta wadanda suka aika wannan aikin takalar fada da ganganci .
973424
captcha