IQNA

Tawagar koyar Da Kur'ani Ta Jeka Da Gidanka Ta Yada Zango A Karamar Jami'ar Gardan Tawun Na Pakistan

15:40 - March 28, 2012
Lambar Labari: 2295499
Bangaren ilimi da nazari: a ranar shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyta ne karamar jami'a ta koyar da kur'ani da ke yankin Gardan tawun na garin Lahur na kasar Pakistan ta fara koyar da karatun kur'ani mai girma a wani salon koyar da ilimin kur'ani na jeka da gidanka.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyta ne karamar jami'a ta koyar da kur'ani da ke yankin Gardan tawun na garin Lahur na kasar Pakistan ta fara koyar da karatun kur'ani mai girma a wani salon koyar da ilimin kur'ani na jeka da gidanka.Ana fara koyar da karatun ne da misalin karfe goma zuwa karfe daya da rabi agogon kasar kuma an samu halartar yan jami'a maza da mata daruruwa da suka halarci wannan koyarwa kuma an koyar das u bangare bangare daban daban na addini tare da nuna gamsuwa da farin cikinsu kan wannan mataki da suka ce ya kayatar da su. Kuma wanna salon koyarwa na bainar jama'a ana gudanar da shi a gaban bainar jama'a a kowane wata.

975374
captcha